IQNA

Musulmin Birmingham Za Su Gudanar Da Sallar Idi

23:36 - August 28, 2017
Lambar Labari: 3481841
Bangaren kasa da kasa, musulmin birnin Birmingham sun sanar da cewa za su gudanar da sallar idin babbar salla a bana kamar yadda aka saba.
Musulmin Birmingham Za Su Gudanar Da Sallar Idi

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na birminghammail cewa, an ajie za a a gudanar da sallar a wani babban wurin shakatawa na birnin.

Babban mai kula da harkokin gudanar da sallar idi na birnin ya bayyana cewa, ana yin kira ga dukkanin musulmi da suke zaune a birnin da su hallara da kimanin karfe bakwai da rabi a wannan wuri.

Ya kara da cewa, bisa la’akari da yanayin cunkoson da ake samu a kan manyan titinua na birnin a lokutan da jama’a suke tafiya aiki da kuma zirga-zirga, a kan ya kamat musulmi da su fito da wuri domin kaucewa haifar da cunkoso.

A kowace shekara musulmin birnin suna gudanar da sallar idi a wannan babban dandali, tare da halartar dubban musulmi.

Baya ga birnin na Birmigham, ana gudanar da sallar idi a sauran biranan da musulmi suke da yawa a kasar ta Birtaniya a kowace shekara.

3635561


captcha