IQNA

Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Cin Zarafin Manzon Allah A Kasar Faransa

23:04 - October 27, 2020
Lambar Labari: 3485312
Tehran (IQNA) Kungiyar Hizbullah ta yi Allah wadai da sake buga zanen batanci ga Manzon Allah (s.a.w.a) da aka yi a ƙasar Faransa.

Kungiyar Hizbullah ta yi Allah wadai da sake buga zanen batanci ga Manzon Allah (s.a.w.a) da aka yi a ƙasar Faransa tana mai cewa sosa ran musulman duniya da kuma yin ɓatanci ga abin da suka fi fifitawa ba ‘yanci ne na faɗin albarkacin baki ba.

kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce ƙungiyar tana nuna tsananin damuwarta dangane da abubuwan ɓatanci da ake bugawa kan Musulunci da kuma Annabi Muhammadu (s.a.w.a) bugu da ƙari kan irin adawar da ake nuna wa addinin Musulunci a ƙasar Faransan.

Sanarwar ta ƙara da cewa: Abubuwan da ake bugawa a ƙasar Faransa suna sosa zukatan sama da musulmi biliyan biyu, ciki kuwa har da al’ummar musulmi da larabawan da suke zaune a Turai da kuma ƙasar Faransa na tsawon shekaru aru-aru.

Hizbullah ta ci gaba da cewa: Dukkanin ikirarin ƙarya na ‘yancin faɗin albarkacin baki ba za su iya halalta cin zarafin Annabi Muhammadu da kuma yin ɓatanci ga saukakkun addinai ba. Don haka ƙungiyar ta kirayi gwamnatin Faransa da ta ɗau matakan hana buga irin waɗannan abubuwan.

Wannan sanarwar dai ta biyo bayan sake buga zane-zane da rubuce-rubuce na ɓatanci ga addinin Musulunci da kuma Manzon Allah (s.a.w.a) da ake yi a ƙasar Faransan ne lamarin da ke ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine daga ɓangarori daban-daban na duniyar musulmi.

3931190

 

captcha